Gwamnatin Jahar Gombe ta karawa Dagatai da Hakimai albashi
Muhammad Inuwa Yahaya gwamanan Jahar Gombe ya amince da a karawa Dagatai da Hakimai albashi.
Ibrahim Dasuki Jalo kwamishina mai kula da harkokin Kananan Hukumomi, ya bayyana haka ga manema labarai a Jahar Gombe.
Jalo yace ” hakan ya faru ne kan irin namijin kokarin da sukeyi a yankunan su, da kuma alkawarin da gwamnatin Jahar Gombe tayi masu lokacin yakin neman zabe.”
KARANTA-Buhari zai kaddamar da aikin Layin dogon da zai tashi daga Kano zuwa Kaduna
” Hakimai da Dagatai za su fara cin moriyar hakan a karshen watan Yuni, in da Hakimai 165 da kuma Dagatai 602 za su ci moriyar hakan.”
“Yanzu duk wata za su sami karin 15,000”
Ya kuma bukaci Hakiman da Dagatan dasu cigaba da bada gudummawa ga yankin su ta ko wanne fanni.
Wakilin Jagoran Hakimai, Alhaji Abdulkadir Abubakar ya nuna godiyarsa matuka ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.
Yace “dafatan sauran Hakimai za suyi anfani da karin albashinnan wajan kara kaimin aiki, da tallafawa gwamnati musamman kan abun da ya shafi tsaro.”
Comments 1