Gwamnatin Jahar Katsina zata miƙa Dajin Kogo domin gina Dandalin Shaƙatawa na Ƙasa
Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya umarci Ma’aikatar Noma data kafa wani Kwamiti da zai kula da miƙa Dajin Kogo a Ƙaramar Hukumar Faskari domin maida shi wurin shaƙatawa na Ƙasa, wanda a cewar sa zai tabbatar da fata aikin cikin sauri.
Gwamna Masari ya bada umarnin a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jami’ai daga Hukumar Kula da Wuraren Shaƙatawa ƙarƙashin jagorancin Dr Okedeji Agboola Okekeyin domin tattaunawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun sace Ɗan Jarida a Zamfara
Masari ya sanar da mutanen da za’a sanya a Kwamitin da su ƙunshi Hakiman Faskari da Sabuwa, Daraktan Daji na Jaha dana Ƙaramar Hukuma da sauran su.
Ya bada tabbacin bayar da dukkanin goyon baya domin ganin an gudanar da aikin cikin nasara.
Gwamnan ya kuma godema Gwamnatin Tarayya data zaɓi Dajin Kogo a Ƙaramar Hukumar Faskari daga cikin Dazuzzuka guda goma da za’a gina Dandalin Shaƙatawa sabbi.
Tunda Farko, Shugaban Gudanar da Aikin Conservator General Dr Okedeji Agboola Okekeyin yace sun zo Gidan Gwamnatin domin sanar da Gwamnan amincewar da Gwamnatin Tarayya tayi na gina ƙarin Dandalin Shaƙatawa guda goma a Ƙasar.
A cewar sa Dajin Hito gogo na daga cikin Dazuzzuka goma da aka amince domin gudanar da aikin.
Yace ziyarar zata kuma basu dama na tattaunawa akan hanyoyin da zasu karɓi Dajin domin shirin gina Dandalin Shaƙatawa.