Gwamnatin jihar Jigawa ta bada umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun jihar bayan fargabar kai hare haren ‘yan bindiga a fadin jihar.
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito cewa An rufe makarantun a yau Laraba yayin da dalibai ke tsaka da zana jarrabawa.
Rufe makarantun cikin gaggawa ya haifar da fargaba ga mazauna jihar da kuma dalibai.
Gwamnan Katsina Ya Halarci Taron Addu’o’in Neman Zaman Lafiya a Kwara
Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar, Wasilu Umar ya tabbatar da rufe makarantun ga manema labarai, sai dai bai yi karin haske ba.
Shima mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce ba rundunar ‘yan sanda ce ta bada umarnin rufe makarantun ba.
Shima a nasa bangaren kwamishinan Ilimi na jihar Dr Lawan Yunusa Danzomo ya tabbatarwa da manema labarai hakan a Ofishinsa.