By Sani Hamza Daudawa April 18, 2021
Gwamnatin Jihar Adamawa ta dakatar da albashin wasu Ma’aikata sama da dubu biyu bayan da aka same su da kin shiga tsarin tantancewa da nadar bayanan Ma’aikata da aka yi a Jihar.
Wannan mataki na zuwa ne daidai lokacin da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Ishaya Dabari da Akanta Janar ɗin Jihar Kefas Tagwi ke ƙaryata maganganun cewa gwamnatin Jihar ta ari kudaden be daga asusun gwamnatin don aiwatar da wasu ayyuka ya sa aka dakatar da albashin.
Tagwi ya ce, ko da yake a baya koti ta yanke hukuncin cewa dole a biya Ma’aikatan basussuka da wasu malamai da aka dauka aiki a shekarar 2012, ya ce kazalika gwamnati ta daukaka kara kan bashin na Naira miliyan dari shida da suke zargin cewa an rike musu.
Kwamishinan Ya ce gwamnatin jiha ta nuna alkunyar ta na kin bayyana ma’aikatan a matsayin na bogi, duk da cewa akwai umurnin kotun.
Ya kara da cewa dakatar da albashin ba ta da nasaba da umarnin kotun sai dai kawai an yi hakan ne don hana samun wani liki a bangaren albashin.