By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya ja kunnen masu hannu da shuni wajen lalata gadun dajin jihar.
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a yayin gudanar da taron tsaro da shugabannin hukumomin tsaro da manyan jami’an gwamnati da shugabannin kananan hukumomi da suka halarta a gidan gwamnati dake Bauchi.
Gwamna Bala Mohammed ya gargadi jami’an kananan hukumomi, sarakunan gargajiya dasu guji yin irin wannan abu, yana mai jaddada cewa, gwamnatinsa za ta yi maganin wadanda aka samu da aikata laifin.
Sannan Yace barnatar da dazuzzukan jihar na daya daga cikin manyan abubuwan dake haddasa rigingimun filaye don haka ya umarci shugabannin kananan hukumomin da su samar da mafita mai dorewa a kan faruwar hakan.
Kazalika Gwamnan ya sake baiwa shugabannin kananan hukumomin gudanar da taron tsaro na yau da kullum tare da hada kan sarakunan gargajiya da ‘yan banga domin tabbatar da ingantaccen tsarin tsaro a kananan hukumominsu.
A cewar sa, “hada kan al’umma shine babban abin da zai hana tabarbarewar tsaro, ya kuma ba su tabbacin ci gaba da bada goyon bayan gwamnatin jihar domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamna Bala Mohammed a wajen taron ya umurci dukkan shugabannin kananan hukumomi ashirin na jihar dasu fara biyan albashin ma’aikatansu a wani bangare na sabuwar dabarar kawo karshen kalubalen da gwamnatin jihar ke fuskanta na biyan albashi.