Gwamnatin jihar Borno za ta kaddamar da wani shiri mai taken “Gwamnatin Jaruman Borno” domin bayar da tallafin karatu ga marayu 500 da matan da aka rasu aka bari da ‘yan Civilian JTF da mafarauta da ’yan banga da suka mutu a yakin Boko Haram da ISWAP.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa shirin zai fara aiki a watan Janairun shekarar 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Larabar nan kuma ya aikawa manema labarai.
“Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ne a jawabinsa na kasafin kudin shekarar 2022 a zauren majalisar dokokin jihar Borno ranar Talata a Maiduguri, in ji sanarwar.
Sanarwar ta cigaba da cewa: “Mun shirya kaddamar da SHIRIN TALLAFIN JARUMAR BORNO. Wannan shirin ya kunshi kafa wata tawagar Gwamnati da za ta zakulo marayun ‘yan sa kai na sibiliyan JTF ‘yan makarantar firamare da sakandare da mafarauta da ‘yan sa kai da suka mutu a lokacin fadace-fadace. Gwamnati za ta bai wa wadannan marayun tallafin karatu ga Kwalejojin Gwamnatin tarayya da sauran Makarantun Duniya. Shirin zai kasance a cikin matakai tare da matakan gwaji na marayu 500.”
“Yawancin wadannan mayakan na sibiliyan JTF, mafarauta da ’yan banga sun rasa rayukansu a fafutukar tabbatar da zaman lafiya a Borno. Insha Allahu muna shirin saka musu bisa irin sadaukarwar da suka yi ta hanyar tarbiyyar ‘ya’yan da suka bari, da kuma tallafa wa matan da suka bari ta hanyar shirin da muke shirin kaddamarwa a watan Janairu, Insha Allahu.” Inji Gwamnan.
Zulum ya bayyana cewa “wani bangare na SHIRIN TAIMAKON JARUMAN BORNO shi ne tantance bukatu na zawarawan da ‘yan agajin da suka rasu suka bari”. Ya yi nuni da cewa “Gwamnati za ta ware tallafin da ake bukata ga wadannan zawarawan domin samun dorewar rayuwa”.