By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Delta ta sake kafa majalisar sarakunan gargajiya, biyo bayan rusa majalisar Obi na Owa, Dokta Emmanuel Efeizomor mai mulki na 11.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Janairu kuma sakataren gwamnatin jihar (SSG), Mista Patrick Ukah ya fitar yace, gwamnatin ta sake kafa majalisar tare da Orodje na masarautar Okpe, Manjo Jar.Felix Mujakperuo (mai ritaya), a matsayin shugaba.
Mujakperuo shi ne mataimakin shugaban majalisar da aka rushe a karkashin jagorancin Efeizomor.
A cikin wasikar, Gwamna Ifeanyi Okowa ya amince da majalisar da aka sake ginawa, tare da Pere na Masarautar Akugbene-Mien, Pere Stanley P Luke, Kalanama VIII, wanda yanzu ya zama mataimakin shugaban farko.
Sabuwar majalisar kuma tana da Obi na Ubulu-Unor, Agbogidi, Obi Henry A. Kikachukwu, a matsayin mataimakin shugaba na 2.
Wasikar ta ce za a kaddamar da majalisar nan gaba kadan.