Wakilinmu Sani Ahamed Bukur
Gwamnatin Jihar Filato, ta Ce ta kashe Naira Miliyan Dari Tara da Ashirin da Biyar wajen daukar Nauyin Mahajjata 630 domin sauke Farali, a Kasa Mai Tsarki.
Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi ga Mahajjatan a filin wasa da ke Jos Babban Birnin Jihar Filato.
Gwamnan ya Kara da cewa munyi haka ne domin Inganta Zaman Lafiya da baiwa kowa hakkin sa a jiha da kasa baki daya.
Kazalika Gwamna Simon Lalong, ya gargadi Mahajjatan da su yi Biyayya ga dukkan dokokin da Hukumar Kasar Saudi Arebiya ta shimfida domin kasancewa Baki Nagari.