Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa gwamnatin jihar ta haramta wa masu babur mai ƙafa uku hawa manyan titunan jihar, a yunƙurinta na zamanantar da shi.
Haramcin zai fara aiki ne daga gobe Litinin, 31 ga watan Agusta.
Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Aisha Sa’idu-Bala, shugabar hukumar tsaftace harkokin sufuri ta jihar Kaduna(KADSTRA), ta ce gwamnati ta fitar da sabon tsari ga direbobin haya a jihar.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamna-el-rufai-ya-sassauta-dokar-hana-fita-a-kudancin-kaduna/
Ta ƙara da cewa an samar da sabon tsarin kula da zirga-zirga a titunan garin domin tabbatar da cewa motoci da kuma babur mai ƙafa uku sun hau titunan da aka sahale musu.
“An yi haka ne domin tsaftacewa da kuma bunƙasa hanyoyin sufuri don kiyaye lafiya da rage cunkoso da kuma tabbatar da an bi dokoki,” kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito.
Titin Kawo zuwa Ali Akilu zuwa Ahmadu Bello na cikin hanyoyin da aka ambata a matsayin haramtattu ga baburan, a cewar Daily Trust.