Gwamnatin Kano ta bada umarnin ci gaba da raba kayan tallafi da kwamitin jihar ya tara a karo na uku.
Amadadin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin karta kwana na yaƙi da cutar Korona a Kano, shi ne ya jagoranci tawagar gwamnatin wajen bikin ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci zagaye na uku wanda aka fara da yankin masarautar Ƙaraye don ci gaba da taimakawa mabuƙata masu ƙaramin ƙarfi wajen rage raɗaɗin wannan yanayi na cutar sarƙe numfashi da duniya ta tsinci kanta a ciki.
Hadimin mataimakin gwamnan Abubakar Musa DK, shi ne ya shaidawa wakilinmu yadda aka ci gaba da rabon kayan tallafin a ranar talata.Haka nan mataimakin gwamnan Dakta Gawuna ya ƙara jagorantar rabon tallafin na Korona wanda gwamnatin tarayya da gammayar kungiyoyi ta Coalition Against Covid-19 (CA-COVID-19) suka samar.
Wanda nan bada daɗewa ba za’a tabbatar wannan kayan abinci sun isa ga mabuƙatan da suke da buƙatar tallafin.