Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na ma taimakin Gwamnan jihar Kano, Hassan Musa wacce aka bayyanawa Manema Labarai ranar 30 ga watan Yulin 2019.
Sanarwar ta ce Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta samu nasarar fadada cibiyoyin kula da cutar Tarin Fuka wanda ake kira TB tare da rage yaduwar ta a tsakanin al’umma.
Yace a shekaru hudun da suka gabata Gwamnatin sa ta samu nasarar kara yawan cibiyoyin kula da cutar tarin Fuka harma a ma’aikatu da hukumomin tsaro.
Shima da yake tofa albarkacin bakin sa, babban Sakataren Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kano Alhaji Usman Bala, yace wannan nasarar ta fadada cibiyoyin yakar tarin Fuka ta samu ne sakamakon wasu ayyukan da aka cimma nasara a kan su ta hanyar hadin gwiwa da wasu kamfanoni.
Suma a nasu jawaban Shuwagabannin kamfanin NAPIMS Jafaru Agyu da na kamfanin “Star Deepwater Petroleum Limited, Rick Kennedy sunce wannan nasara da aka samu tana nuna cewa akwai kyakkyawan alaka tsammanin Gwamnatin jihar da sauran bangarorin kawo cigaba.
Sun ce karamin asibitin kirji da bangarorin suka baiwa gwamnati a matsayin gudummawa za taimaka gaya wajen Yakar Cutar.