Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa, jihar a shirye take ta shirya addu’o’in kasa duk shekara domin neman tsarin Allah da kuma shiriya ga kasa da jihar baki daya.
“Muna bukatar mu tsaya tsayin daka wajen neman taimakon Allah domin kare lafiya da tsaron kasarmu ta uwa ta Najeriya, da kuma jihar da muke kauna,” in ji Ganduje.
Wannan addu’a ta kasa da ake gudanarwa a karkashin Jagorancin Jagoran Darikar Tijjaniyya na Duniya, Khalifatul Amm Lidariqatul Tijjaniyya, Sidi Sharif Ali Bin Arabi, mai albarka, duba da irin girman malaman addinin Musulunci na ciki da wajen kasar nan, wadanda suka halarta, Ganduje ya ce, a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar ya fitar kuma ya aika mana.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Bin Arabi ne ya jagoranci zaman addu’ar, wanda ya taho daga kasar Aljeriya tare da rakiyar fitattun mutane. Wadanda suka hada da shugabannin Zawiyya na Aljeriya, da wakilin shugaban kasar Aljeriya da kuma malaman jami’o’i.
Sanarwar ta ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kuma halarci bikin, tare da Mukaddamai da Limamai da Huffaz da kuma Muridai da dama.
‘’ Gwamna Ganduje ya ce, “A shirye muke mu shirya addu’o’in shekara a jihar. Domin muna matukar bukatar taimakon Allah daga wurin Allah domin rashin tsaro da ya dabaibaye al’ummar kasar.”
“Ina so in yi amfani da wannan dandali wajen neman mai girma Sheikh Dahiru Usman Bauchi cewa Kano tana son karbar bakuncin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass na bana. Muna son yin nisa wajen ganin mun kara kulla alaka a tsakaninmu,” in ji Ganduje a cikin sanarwar.
A cewar sanarwar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya bayar da wannan bukata, a lokacin takaitaccen jawabinsa na cewa, “an yi la’akari da abin da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nema.
‘’ Zaman addu’ar ya samu halartar wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne karamin ministan noma, Mustapha Baba Shehuri, da daukacin majalisar ministocin gwamnan da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Kano, injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.’’.