Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ya ce jihar ta kashe Naira biliyan huɗu da Miliyan 270 daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa Agustan 2020 a kan harkar tsaro.
Ya bayyana hakan ne a Katsina yayin da yake yi wa ’ya’yan ƙungiyar ’yan Jaridu ta ƙasa (NUJ) jawabi ranar Litinin.
Sakataren ya ce gwamnati ta kashe kuɗaɗen ne ƙarƙashin ofishinsa wajen samar da kayan aiki da kuma biyan kuɗaɗen alawus ɗin jami’an tsaro.
Ya ce sun kashe Naira 691 daga watan Yuni zuwa Disambar 2015; miliyan 827 daga Janairu zuwa Disambar 2016; miliyan 749 daga Janairu zuwa Disambar 2017 da kuma Naira miliyan 590 daga Janairu zuwa Disambar 2018.
https://dimokuradiyya.com.ng/sojoji-sun-kashe-yan-bindiga-100-a-yankin-katsina-da-zamfara/
Mustapha Inuwa ya kuma ce sun kashe Naira miliyan 682 a shekarar 2019, sai kuma Naira miliyan 732 daga Janairu zuwa Agustan 2020.
Ya ce gwamnatin jihar na kashe kuɗaɗen ne wajen ƙarfafa gwuiwar jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
“Gwamnatin Katsina tana ɗaukar nauyin ayyukan jami’an tsaro tun daga rundunar tsaro ta Operation Sharar Daji na rundunar sojojin Najeriya shiyyar ta ɗaya a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara da Neja.
“Amma daga bisani kowace jiha ta ɗauki nauyin samar da ofisoshi da wuraren zaman jami’an da aka tura yankinta.
“Muna gyarawa, saye, da zuba mai ga motocin rundunonin tsaro na Operation Mesa, Operation Kan ka ce Kwabo, Operation Dirar Mikiya, Operation Sahel Sanity da dai sauransu”, inji Inuwa.