By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kogi ta haramta yin hakar gawayi a kananan hukumomi 21 na jihar.
Kwamishinan Muhalli na jihar, Victor Omofaiye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a ranar Juma’a.
Omofaiye ya bayyana cewa hakar gawayi a jihar ya sabawa doka kuma an haramta yin sa baki daya.
Ya yi gargadin cewa duk wani mutum ko gungun mutanen da aka kama suna yin gawayin ko mallakar kayan da ake yin gawayin za a kama su kuma a gurfanar da su a gaban kotu.
Sanarwar ta kara da cewa “Duk motar da aka kama tana dauke da gawayi gwamnatin jihar Kogi za ta kama ta.”
A zantawarsa ta wayar tarho da wakilinmu kan dalilin dakatarwar, kwamishinan ya ce hanya ce ta kiyaye muhalli ta hanyar hana sare bishiyu.
“Shin kuna farin ciki da yadda ake lalata muhallinmu? Ba za mu iya naɗe hannayenmu mu kalli yadda ake lalata muhallinmu don son kai ba.
Omofaye ya kara da cewa “Gwamnati na da alhakin daukar matakin dakile gurbatar muhalli.”