Gwamnan Jihar Ondo Mista Rotimi Akeredelu ya tsagaita dokar hana fita da aka kakaba a yankin Ikare-Akoko biyo bayan wata tarzoma da ta barke kwanakin baya.
Tarzomar ta barke ne kan wani rikicin Kujerar sarautar yankin, lamarin da ya kai gai gwamna Akeredelu ya kafa doka hana fita na sa’o’i 24, ro amma a yau Lahadi ya tsagaita dokar daga karfe bakwai na almuru zuwa bakwai na safiya.
Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Mista Donald Ojogo ya fitar, ta ce gwamnati ta dauki matakin tsagaita dokar ne biyo bayan ganin irin yadda kura ta lafa a yankin.
Sai dai Sanarwar ta ce idan har jama’a suka kuskura suka sake gutsuro wata fitina, to lashakka za a sake komawa yar gidan jiya.
Sanarwar “Gwamnatin Jihar Ondo ta nazarci yanayin dokar hana fita da ta kakaba a yankin Karamar hukumar Ikare-Akoko ta arewa maso gabas”
“Don haka gwamna Akeredelu ya bada dama wa jama’a daga ranar Litinin 10 ga watan Mayu za a tsagaita dokar daga karfe bakwai na almuru zuwa bakwai na safiya”
Daga bisani ya ja hankalin jama’a da su zamo masu bin doka da oda don zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.