Gwamnatin Jihar Kwara ta ba da tabbacin cewa ma’aikata a fadin jihar sun nuna kalubalan su game da fama da matsalar biyan albashi inda ta tabbatar musu da cewa taji korafin su kuma zata share musu kukan su. Kwamishinan sadarwa, na Gwamnan Alhaji Mohammed Sabi Ishak shine ya bada tabbacin hakan lokacin da yake wata hira da manema labarai a garin Ilorin. Alhaji Ishak wanda ya nuna damuwar sa akan rashin biyan wannan albashin inda ya dora laifin ga ‘yan majalisar jihar ganin yadda basa nuna damuwar su game da lamarin. Ya bayyana cewa an sake fasalin mai kyau wajen taimakwa ma’aikatan domin za su rinka samun albashin su a lokaci guda ba tare da samun tsaiko ba. Alhaji Ishak ya ce” matsalolin za suzo karshe ne da zarar an zartar da sabon tsarin da aka fito da shi wajen biyan albashin ma’aikatan. Ya lura cewa halin da ake ciki wani yana yi ne na damuwa inda ya nuna rashin jin dadinsa, ya kara da cewa Gwamnan yana jin damu sosai game da batun ma’aikata. Kwamishinan ya bukaci ma’aikata su yi hakuri kuma suyi aikin su sabida Allah, ya kuma yaba musu da goyon bayan da suke bawa gwamnatin ta yanzu da kuma kiyaye zaman lafiya a wurin aikin su. Alhaji Ishak duk da haka ya bukaci ma’aikata su nuna gamsuwa ga gwamnatin mai zuwa.