Gwamnatin jihar Oyo ta sassauta dokar kulle da ta saka don dakile yaduwar cutar sarke numfashi a jihar.
Gwamnati ta ce daga ranar 29 ga watan Yuni da muke ciki, duk ma’aikatan jihar su dawo bakin aikinsu.
” Sannan kuma yaran makarantu daga aji 6, JSS 3, SS 3 su dawo domin ci gaba da karatu.”
Sakataren yada labarai na jihar Taiwo Adisa ne, ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai ranar Litini. Sannan muatne za su ci gaba da walwala tun daga karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare.
Ya kuma ce wuraren ibada a jihar za su ci gaba da ibada kamar yadda aka saba a da sai dai kuma za a bi ka’idojin da gwamnati ta saka na kariya daga kamuwa da Korona.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta amince wa ma’aikata daga mataki na 13 zuwa sama, da su fara zuwa aiki tun a ranar 27 ga watan Afrilu. Amma yanzu gwamnati ta bude duk ofisoshi domin duk ma’aikatan su dawo bakin aikinsu a Litini 22 ga watan Yuni.
“Duk daliban da gwamnati ta amince su fara karatu za su saka takunkumin fuska, wanke hannaye da amfani da man tsaftace hannaye.