A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani kan korar malaman firamare 2,357 a fadin jihar.
A makonnin da suka gabata ne gwamnatin jihar ta kori malaman firamare sama da 2,000 saboda rashin iya aiki da kuma rashin cancantar koyarwa.
Haka kuma ta kori shugaban kungiyar malamai ta kasa saboda rashin halartar jarabawar cancantar da bai yi ba.
Da yake mayar da martani, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna, KADSUBEB, Tijani Abdullahi, a ranar Litinin, ya bayyana cewa korar malaman da ake zargin ba su cancanta ba ne kuma an yi hakan ne domin bunkasa ilimin firamare a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta kori malamai sama da 2000 ne saboda tana son a samu ilimi mai inganci, da inganta ayyukan kungiyar malamai ta kasa NUT.
Shugaban SUBEB a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai kan matsayar gwamnati a kan lamarin ya bayyana cewa akwai shirin daukar Malamai Dubu Goma domin magance babban gibin da ake samu a bangaren Malamai, dake kuma koyar da dalibai..
A wani labarin kuma na daban.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya, CJN.
An rantsar da Ariwoola a ranar Litinin a zauren majalisar da ke Abuja.
Ya karbi mulki daga hannun tsohon CJN, Ibrahim Tanko Muhammad wanda ya yi murabus a ranar Litinin saboda rashin lafiya.
An haifi Mai shari’a Ariwoola ne a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1958 kuma a halin yanzu shi ne babban alkalin kotun koli.
Tsohon Alkalin Kotun Daukaka Kara ne kuma an daukaka shi zuwa Kotun Koli bayan sauya shekarsa daga Babbar Kotun Jihar Oyo.
Ariwoola ya fara karatunsa ne a garinsu Iseyin a makarantar Muzahara ta karamar hukumar Oluwole a karamar hukumar Iseyin ta jihar Oyo tsakanin shekarar 1959 zuwa 1967.