A ranar Lahadin nan ne gwamnatin jihar Kaduna ta nisanta Kanta da labarin wani faifan bidiyo da ake yada a wa Kuma ke nuna jami’an tsaro na kama wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Chikun.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar, a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, ya ce sun samu tambayoyi daga manema labarai da al’uma a kan bidiyon.
A cewarsa, ya zama dole a fayyace cewa gwamnatin jihar ba ta samu martani daga hukumomin tsaro ba dangane da irin wannan aiki.
Sanarwar ta ce “Saboda haka ba za a iya bayar da wani bayani ba a wannan lokacin kan sahihancin faifan bidiyon da ke zagaye Kafafen yada labarai na zamani.
“Gwamnatin jihar Kaduna tana jiran tabbaci faruwane hakan daga hukumomin tsaro kan ayyukan da ake gudanarwa a wurare daban-daban dake fadin jihar Kaduna. Da zaran an sami cikakkun bayanai na aikin, za a ba da cikakken bayani ga manema labarai da ‘kuma al’umar kasar nan,” in ji sanarwar