Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa, za ta fara bude makarantu daga ranar Laraba, 18 ga watan Ogustan shekarar 2021.
Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Shehu Usman Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Inda sanarwar ta bayyana cewa, daliban da ke karamin aji na sakandare wato JSS III ne kadai za su koma makarantun.
Kazalika sanarwar ta yi nuni da cewa, daliban da za su koma makarantun da kayan gida za su rika zuwa a maimakon kayan makaranta da aka saba amfani da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babbar Yar Tsohon gwamnan Yobe ta rasu
“Gwamnati ta bada umurnin bude makarantu ga daliban JSS III, wadanda za su rubuta jarrabawar su ta NECO BECE, da za fara a ranar 23 ga watan Ogusta, zuwa 6 ga watan Satumba shekarar 2021” inji sanar war.
“Don haka, ana umurtar bude makarantun sakandare, domin daliban JSS III daga ranar 18 ga watan Ogustan 2021, kuma a na sanar da daliban su rika zuwa da kayansu na gida.”
Comments 1