Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da ke jihar da su yi koma Bude makarantun sai hudu kacal a mako guda Mai makon sau biyar da aka Saba, yayin da za a bude makarantu a ranar 10 ga watan Janairu a zango na biyu na shekarar 2021/2022.
Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal ce ta ba da wannan umarni a Kaduna ranar Lahadi a cikin sanarwar da ta ce, za a ci gaba da karatun zango na biyu na shekarar 2021/2022 kamar yadda aka tsara a baya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa gwamnatin jihar Kaduna a ranar 1 ga Disamba, 2021, ta fara sauya ranakun zuwa aikin Ma’aikatan jihar daga Kwanaki biyar zuwa hudu a duk mako.
Wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai ya fitar, ta bayyana cewa sabon matakin zai shafi kamfanoni masu zaman kansu daga karshe.
A cewar sanarwar, an tsara matakin ne don taimakawa wajen haɓaka aiki, inganta daidaiton rayuwar aiki da baiwa ma’aikata damar samun ƙarin lokaci ga iyalansu, don hutawa, da kuma samun cikakkiyar damar gudanar da aikin gona.
Miss Lawal ta bayyana cewa bisa la’akari da sabon ci gaban da aka samu, za a daidaita Jadawalin karatu a jihar Kaduna ta 2021/2022 don tabbatar da daukar nauyin manhajar karatun.
Ta ce ya kamata dukkan iyaye, masu riko da kuma sauran jama’a su lura cewa gwamnatin jihar ta amince da ranar 10 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a ci gaba da karatu a makarantun jihar a zangk na 2, na shekarar 2021/2022.