Gwamnatin jihar Kaduna ta nesanta kanta da hannu a sace Abubakar Idris Usman, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda aka sace shekara guda a jihar kuma har yanzu babu labarinsa.
Shekara ɗaya bayan ɓacewar tasa da ake zargin gwamnatin jihar da hannu amma ba ta ce uffan ba, ma’aikatar sharia’arta ta ce gwamnatin jihar ba ta da masaniya ko hannu a ɓacewar Dadiyata wanda ya yi fice wajen sukar gwamnati.
“Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kaduna na faɗa da babbar murya cewa gwamantin jihar Kaduna ba ta da masaniyar inda Abubakar Idris Usman wanda aka fi sani da Dadiyata yake ko hannu a ɓacewarsa.
“Duk wani tunani saɓanin haka to ƙoƙari ne na cewa gwamnati na da hannu saboda a cikin jihar Kaduna aka sace shi”, inji kwamishinar Shari’a, Aisha Dikko.
Ta ce gwamnatin jihar ba ta taɓa kai ƙorafin Dadiyata wurin ‘yan sanda ba ko kuma shigar da ƙararsa a gaban kotu.
A shekarar 2019 ne wasu ’yan bindiga suka ɗauke Abubakar wanda malami ne a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutisn Ma, bayan ya dawo gidansa da ke a unguwar Barnawa, Kaduna cikin tsakar dare.
Tun daga lokacin ba a sake jin ɗuriyarsa ko ganin motarsa da ’yan bindigar suka tafi da shi a cikinta ba.
Rahotanni sun ce Dadiyata na cikin yin waya ne bayan isowarsa gida kafin ya shida ɗaki ’yan bindigar suka ɗauke shi da ƙarfin tsiya suka sa a cikin motarsa sannan suka tafi da shi.
Sanarwar da kwamishinar ta fitar na martani ne ga ƙorafin da ya kai ga janye gayyatar da aka yi wa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a matsayin mai jawabi a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA).
Ƙungiyar ta soke gayyatar ne bayan wasu ’ya’yanta sun zargi Gwamna El-Rufai da tauye hakkin dan Adam da gazawa wajen magance kashe-kashe a kudancin jiharsa da kuma da saɓa umarnin kotu na sakin mutanen da ke tsare.
Da take magana game da waɗanda ke tsaren, Aisha Dikko ta ce dukkannin batutuwan da suka shafi manyan laifuka “na kamanceceniya da juna wurin tunzura jama’a da yaɗa bayanan ƙarya da babu wata wayayyiyar al’umma da za ta lamunta, ballantana a jihar da ta sha fama da rikice-rikicen ƙabilanci da addini”.