Hukumar kula da ilimin firamare na jihar Kaduna (SUBEB) ta kammala shiri tsaf domin saka yara 145, 000 wanda ba su da ilimin boko a makarantun firamare a jihar. Mataimakin shugaban hukumar Ibrahim Aminu ne ya sanar da haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a garin Kaduna a ranar Laraba.
Aminu ya ce hukumar ta horas da ma’aikata 2,000 da za su wayar da kan iyayen da ‘ya’yan su ba su da irin wannan ilimin mahimmancin saka ‘ya’yansu a makarantun firamare. Ya ce wannan shiri na saka yara a makarantun firamare na karkashin shirin samar da ilimin firamare na babbar bankin duniya (BESDA) sannan burinsu shine saka yaran da basu da ilimin boko 727,764 a makarantun firamare nan da shekara 10.