Gwamnatin Jihar Kano da shirin bunkasa noma na APPEALS sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wata Makarantar Aikin Noma dake kasar Morocco Mai suna (Ecole National D’ Agriculture).
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an sanya hannun ne da nufin saukaka yada za’a gudanar da aiyukan noma na Zamani a jihar Kano.
KU KARANTA: Dalilin Da Ya Sa Cin Hanci Da Rashawa Ke Kara Tabarbarewa A Najeriya – Jonathan
Sauran bangarorin da aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar sun hada da; inganta Ilimin wadanda zasu ci gajiyar shirin, ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki da sauran abokan hulɗa.
A yayin bikin sa hannu a yarjejeniyar da aka gudanar a makarantar koyon aikin gona ta Meknes da ke kasar Morocco, kwamishinan harkokin noma da albarkatun kasa na jihar Kano Dr. Yusuf Jibril Rurum, shi ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar Kano yayin da Farfesa Sa’id Amiri a madadin makarantar bunkasa noma ta Morocco, dukkansu sun bada tabbacin ganin da an cimma nasarar yarjejeniyar da aka yi a gaban kodinetan ayyukan APPEALS na kasa Mista Jobdi Muhammad.
Sauran wadanda suka shaida Sanya hannun a yayin taron sun hada da Manajan Daraktan Hukumar Noma da Raya Karkara (KNARDA) na Kano Dr. Junaid Yakubu, sai mai baiwa Gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin noma Alh. Hafiz Muhammad, kodinetan ayyukan APPEALS na jiha Dr. Hassan Ibrahim, daraktoci daga ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jiha, wakilan ofishin APPEALS na kasa, masu ba da shawara da sauran masu ruwa da tsaki.
A wani labarin kuma; Kuyi watsi da Dokar IPOB — Gwamnatin Anambra
Gwamnatin jihar Anambra ta bukaci ƴan asalin kasarta da su yi watsi da zanga-zangar zaman dirshan da wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB suka sanar.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Paul Nwosu ya fitar ya ce an jawo hankalin gwamnatin jihar kan sanarwar da ya bayyana a matsayin mugu, mara hankali, koma baya da kuma azabtar da ba dole ba.
Ya ce umarnin da aka fitar a shafukan sada zumunta na “makiya al’ummar Igbo ne.