Gwamnatin Kano ta Baiwa Ɗalibin Da Yafi Kowa Maki a JAMB Tallafin Karatun Miliyan 3
Gwamnatin Jihar Kano ta baiwa wani Ɗalibi dan asalin Jahar, Suyudi Sani tallafin karatu na Naira miliyan 3, bisa nasarar da ya samu a jarrabawar da UTME inda ya samu maki 303 cikin 400.
Da take jawabi yayin gabatar da tallafin kuɗin, kwamishiniyar ilimi mai zurfi, Dakta Mariya Mahmud Bunkure, ta ce Sani, wanda tuni ya samu gurbin shiga jami’ar Bayero ta Kano (BUK), shi ma a kwanan baya ya halarci gasar masana Kimiyya na Najeriya inda ya zo na 7 a cikin mutane 774 da suka fafata a gasar daga ko’ina cikin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba za ka bar APC ba – Shettima ga Tsohon Gwamna Bindow
Ta kara da cewa, “Baya ga Suyudi ya zo na daya a fannin Biology a waccan gasar, shi ma ya zo na daya a gasar matasan masana kimiyya a matakin jiha, wanda ya ba shi damar shiga takarar gasar na ƙasa.”
Bunkure ta ce irin nasarorin da ya samu a hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ta UTME ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin mara masa baya da bashi tallafi
Ta ce baya ga kudaden da aka baiwa wanda ya lashe kyautar, gwamnati kuma za ta dauki nauyin daukar nauyin karatunsa gaba daya domin ganin cewa karatunsa bai shiga wani hali ba.
Bunkure ta kuma ce gwamnati ta yanke shawarar bikin karramawar ne domin ya samu kwarin guiwa da kwadaitar da shi a nan gaba da kuma zama abin koyi ga sauran daliban jihar.
Ta kara da cewa gwamnatin Ganduje za ta ci gaba da mai da hankali sosai kan ilimi domin ƴan Jahar ta su samu digiri na jami’a.
Wanda aka baiwa Tallafin karatun, ya godewa gwamnatin jihar bisa wannan karamci da suka yi masa, sannan ya yi alkawarin kula da maida hankali akan karatunsa