Gwamnan ne ya bayyana hakan a jiya wajen Bukin ranar ma’aikata Wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha, dake Birnin kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace yayi hakan ne Dan samun ingantuwar ma’aikatan jahar, da kuma kudurin da Gwamnatin sa ke da shi na Ceto Rayuwar Ma’aikata.
Kazalika ya cigaba da jaddada wa ma’aikatan Aniyar sa kan mafi karacin Albashi na Naira 30.000. Inda ya ce sun shirya Tsaf Dan tabbatar da hakan. kuma ya kara da cewa ma’aikata za su yi walwala, cikin Nishadi, da Alfahari da Gwamatin Jihar Kano.
A gefe Guda kuwa Shugaban Kwadago na jihar Kwamared Kabiru Minjibir, ya yaba da kokarin Gwamnatin inda yace a biya ma’aikata alawus da kuma malamai na manyan Makarantu Dan yayi dai dai da kudurin Gwamnatin tarayya.