• Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da tarukan bukukuwan sallah a fadin jihar.
• Sai dai gwamnatin ta amince a yi sallar Idi a dukkannin Masarautu biyar dake jihar, da kuma masallatan.
• Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanar wa da ya fitar a yau, inda kuma ya shawarci al’umar da su kula matuka da kdokokin Kariya daga kamuwa da cutar Covid-19.
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da dukkanin dau’in bukukuwan Babbar Sallah a fadin jihar baki daya, domin yin amfani da ankarar da jihohi 6, ciki harda Kano, kan kara samun rahotonnin barkewar cutar Korona da gwamnatin tarayya ta yi.
Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a yau Litinin, a cikin wata sanarwa da ya fitar. Inda ya ce za’a a iya gudanar da sallar Idi a dukkannin Masarautu biyar dake jihar, da kuma masallatan dake fadin jihar.
Ya ce an dauki wannan matakin ne, bisa ganin yadda Nigeria ke sake fuskantar barkewar cutar COVID-19 a karo na uku, bayan samun barkewar kwayar cutar Mafi hadari a jihar Delta.
KARANTA WANNA LABARIN: Kutu ta dakatar da yan majalissar dokokin jihar Zamfara kan yunkurin su na tsige Mataimakin Gwamnan jihar
Malam Garba ya ce, ankararwar da gwamnatin tarayya ta yi, ya sanya jihohin da lamarin zai ka iya shafa, daukar matakan kariya na takaita taruwan mutane a wuri guda, musamman ma a bikin gargajiya na Hawan Sallah, Wanda ake yi wa dawakai ado, da kuma taruwar mutaniu upe su na kallon yadda ake Hawan dawakan.
A karshe kwamishinan ya shawarci al’umar baki daya, da su tabbatar da sun bi ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar Korona, da su ka hadar da: Sanya takunkumin fuska, ya waitar wanke hannu, da kuma bada tazara a lokacin gudanar da sallar Idi.