Kwamitin da gwamnatin Kano ta dorawa alhakin kula aikin inganta wutar lantarki a jihar ya tabbatar da cewa nan da wata guda za’a kammala aikin samar wutar megawat 7 da rabi don amfanin al’umma.
Mataimakin shugaban kwamitin Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi shine ya bada tabbacin a yammacin Asabar din nan, yayin da kwamitin karkashin jagorancin shugaban ma’aikata na jihar Kano kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Usman Bala ya kai ziyarar duba aiki tashar wuta dake Dam din Tiga da gwamnatin Kano ke aikin samarwa.
KU KARANTA: Osinbajo Ya Shilla Kasar Vietnam Domin Yin Ziyarar Kwanaki Uku
Yace idan aikin ya kammala zai bada isashshiyar wuta a titunan jihar nan da kuma kara samar da ita ga sauran sassa wanda hakan a cewar sa zai kara bunkasa tattalin arzikin al’umar jihar Kano.
Rabi’u Sulaiman Bichi ya kara da cewa gwamnatin Kano zata samar da wutar ne kari akan megawat 300 da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar nan a yanzu haka wannan kwamiti ke kokarin aikin janyo wa daga Kumbotso zuwa Rimin Zakara.
Ya kuma ce tun da fari gwamnati ta dauki aniyar samar da megawat 15 ne sai dai hakan ba zai yiwuba sakamakon yanayin Dam din ke ciki na bukatar yasa wanda hakan ya rage karfin zuwan ruwan.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa daga cikin wadanda suka ziyarci tashar wutar akwai shugaban ma’aikatan jihar Kano Usman Bala, da shugabar kamfanin wutar lantarki na Kano Injiniya Hadiza Ahmad Tukur da sauran jami’an gwamnati.
A wani labarin kuma: 2023: Wasu Tsofaffin Shugabannin Kasa Guda Biyu Suna Goyon Bayan Peter Obi – Utomi
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Pat Utomi, ya yi ikirarin cewa wasu tsoffin shugabannin kasa guda biyu magoya bayan dan takarar shugaban kasa ne na jam’iyyar Labour LP, Peter Obi.
Utomi ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a wani taro a ranar Juma’a, wanda kungiyar Yell Out Nigeria for Good Governance ta shirya a Abuja.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa Utomi bai bayyana sunayen tsoffin shugabannin kasar ba.