By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Kano ta fara juyar da filayen da ba a amince da su ba, zuwa manyan makarantu
Dangane da kalubalen tsaro da ake fama da shi da kuma cunkoso a makarantun da ke wajen birnin, gwamnatin jihar Kano ta fara soke kadarorin da aka mallaka ko kuma ba a rubuta su yadda yakamata ba a cikin manyan birane don kafa manyan makarantun sakandare.
Matakin na nufin rage cinkoso a makarantun kwana dake cikin kananan hukumomi 36 wannan ya biyo bayan sace dalibai a makarantun kwanan dake makwabta jihohi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya rabawa manema labarai a Kano ranar Litinin.
Ya ce a halin yanzu gwamnati na bibiyar lamuran tsaro yayin da ake fuskantar hare -hare ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a dazukan da ke makwabtaka da jihar, don haka gwamnati za ta tashi tsaye wajen daukar matakan da za su tabbatar da tsaro a makarantun ta.