Gwamnatin jihar Kano ta gargadi manoman jihar da su daina amfani da sharar masana’antu a matsayin taki, tana mai cewa hakan na haifar da munanan cututtuka.
Kwamishinan Muhalli, Dr Kabiru Ibrahim Getso, ne ya yi wannan gargadin a wani taron manema labarai a Kano, ya jaddada cewa amfani da sharar masana’antu a matsayin taki na da illa ga lafiya, da kuma haifar da cutar koda.
A cewar kwamishinan, yankunan da manoma suka fi yin wannan Abu, sun hada da Wudil, Tamburawa, Dawakin Kudu da Gezawa.
Ya kuma yi kira ga mutanen da ke zaune a kusa da wuraren masana’antu irin su Sharada da Challawa da su yi taka-tsan-tsan tare da kaucewa cudanya da sharar masana’antu.