Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta rufe kwalejojin fasahar kiwon lafiya masu zaman kansu guda 26 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na jihar.
Yaduwar makarantun a baya-bayan nan, a cewar gwamnatin jihar, yana da illa ga lafiyar jama’a, ci gaban ilimi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/yanzu-yanzu-kotu-ta-hana-amotekun-shiga-ayyukan-samar-da-tsaro-a-zaben-gwamnan-jihar-osun/
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da rufewar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar lafiya ta jihar, Hadiza Namadi,wanda kuma ta rabawa manema labarai a ranar Juma’a.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar ta lura da matukar damuwa, yadda ake ci gaba da samun yaduwar cibiyoyin horas da lafiya masu zaman kansu (PHTIs) ba bisa ka’ida ba a jihar ba tare da bin ka’idojin kafawa da kuma gudanar da irin wadannan makarantu ba kamar yadda hukumomin gwamnati da suka dace da sauran su suka bayyana.
“Abin takaici ne matuka ganin cewa wasu daga cikin wadancan cibiyoyin da ba a san su ba ba su da takamaiman wurare kuma suna ba da shirye-shirye na shakku kan tsarin karatun da aka kafa, tare da karbar makudan kudade ga dalibai da iyayensu.
“Saboda haka, ana sanar da jama’a game da rufe dukkanin cibiyoyin horar da lafiya ba bisa ka’ida ba (HTIs) a cikin jihar nan take, har sai an kammala cikakken binciken da ya dace.”
Makarantun da aka garkame wadanda abin ya shafa sun hada da:
- Unity College of Health Science & Technology Dorayi Karama (K.G/Mai), dake karamar hukumar Gwale da karamar hukumar Danbatta.
- Khalil College of Health Science & Technology dake kan titin Zaria daura da Gadar Lado Darmanawa
Unguwa Uku daura da Ofishin Hisbah, Karkasara,daura da Masallacin Bilal, dake karamar hukumar Tarauni; karamar hukumar Danbatta; da kuma karamar hukumar Wudil. - Shamila College of Health Science & Technology dake karamar Gezawa.
- Autan Bawo College of Health Science & Technology dake karamar hukumar Rano.
- Trustee College of Health Science & Technology Jakara,a karamar hukumar Dala – Kano
Bachirawa, da karamar hukumar Ungogg – Kano. - Eagle College of Health Science & Technology, karamar Bichi.
- Albakari College of Health Science & Technology, Rijiyar Zaki,karamar hukumar Ungoggo – Kano.
- Jamatu College of Health Science & Technology, karamar hukumar Kura.
- Savanna College of Health Science & Technology, karamar hukumar Wudil.
- Institute of Health Education
Ahmadiyya, daura da Ofishin hukumar zabe INEC. - Jamilu Chiroma College of Health Science & Technology
Kings-Garden, daura da titin Zungeru, Titin filin jirgin sama, Sabon Gari - Sir Sanusi College of Health Science & Technology
dake kan titin Matan Fada. - Aminu Ado Bayero College of Health Science & Technology
Ado Bayero Layout, Dandinshe Yamma –karamar hukumar Dala. - Awwab College of Health Science & Technology, Salanta, karamar hukumar Gwale.
- Gwarzo Unity College of Health Science & Technology, karamar Gwarzo.
- Al-wasa’u College of Health Science & Technology, Tudun Fulani, karamar hukumar Nassarawa – Kano.
- Kanima Academy, Layin Dan-kargo, Zangon Dakata, Karamar Hukumar Nassarawa – Kano.
- Muslim College of Health Science & Technology, dake kan titin Zungeru,karamar hukumar Fagge – Kano.
- Utopia College of Health Science & Technology, Jigirya JSS, Yankaba, Karamar Hukumar Nassarawa – Kano
- Jama’a College of Health Science & Technology, Na’ibawa Yan-lemo,Karamar hukumar Tarauni – Kano.
- Kausar Healthcare Academy, kan titin Jos kusa da Islamic Centre,Karamar hukumar Tudun Wada – Kano.
- Shanono College of Health Science & Technology, lamba 33 Kofar Gari, karamar hukumar Shanono – Kano.
- Institute of Basic Health Education, Jakara Garden,kan titin jigin sama, karamar Nassarawa – Kano.
- Makarantar Fasahar kiwon Lafiya, Habib Faruq Girls Sec. Sch., Gidan Kara, Kurna T/Fulani.
- Makarantar Fasahar kiwon Lafiya, Makarantar Firamare ta Musamman Bachirawa, karamar hukumar Ungoggo.
- Fudiyya School of Health Sciences, Danrimi, ‘Yan-babura Rijiyar Lemo, Karamar Hukumar Fagge.