Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da aikin babura masu kafa uku wadanda akafi sani da A daidaita Sahu bayan karfe goma na dare daga ranar Alhamis 20 ga watan Yuli.
A sanarwar da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammadu Garba ya fitar yayi nuni da cewa an dau matakin ne bayan kammala taron majalisar tsaro ta jihar Kano.
Ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar.
Kwamishinan cikin sanarwar ya bukaci ‘yan Sahu subi dokar yayin da jami’an tsaro zasu tabbatar da anyi biyayya ga umarnin.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa yanzu haka ana ci gaba da samun masu aikata muggan Laifuka, da fashi da makami, ta hanyar amfani da babu din mai kafa uku.
Abun jira a gani shine, yadda dokar zata fara aiki, kasancewar baburin ne kaɗai abun zirga zirga, da akan yi amfani da shi a jihar da daddare.