Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce Gwamnatinsa taa bayar da himma wajen ganin ta zamantar da harkar kiwo da Fulani ke Yi a Jihar baki daya.
Gwamnan ya ce tuni suka Samar da wani shiri a Dànsoshiya dake karamar Hukumar Kiru, Hadin Gwiwa da bankin Islama inda aka Samar da gidaje da kuma Babban Dam saboda Ruwa Sha.
Dr Ganduje ya bayyana hakan ne a Kadawa dake karamar Hukumar Garin Mallam, yayin kaddamar da Huji ga Shanun Makiyaya guda Miliyan 1, baya ga dabbobi, Wanda kuma za a ci gaba da yinsa a daukacin Kananan Hukumomin Kano 44, inda za a shafe makwanni hudu ana aiwatarwa.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa sun dauki Matasa da suke da sani a fannin kimanin su 220 domin ci gaba da Gudanar da aikin Hujin da kuma baye ga sauran dabbobin Makiyaya dake fadin Jihar Kano.