Majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa fitaccen malamin addinin Islama na jihar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa’azi a dukkanin faɗin jihar nan take.
Tare da shaidawa kafafen watsa labarai na jihar dakatar da dukkanin wani wa’azinsa da suke sanyawa a gidajen rediyo. Inda gwamnatin ta ce ta yi hakan ne saboda dalilan tsaro.
Sai dai ta ce dakatarwar ba na dindindin bane, ta kafa kwamiti da zai yi bincike, wanda da zarar an kammala binciken, za a fadi sakamakon binciken bisa zarge-zargen da ake yi wa Shaikh Abduljabbar din.