Gwamnatin jihar Kano ta ki amincewa da sauya ma’aikatan gwamnati 5 da ke neman mika aikinsu ga wasu mataimakan, sannan ta amince da karin girma ga ma’aikatan gwamnatin 175 a cikin watan Nuwamba, shekarar 2021da muke ciki.
Shugaban Hukumar kula Ma’aikatan Kano injiniya Bello Mohammad Kiru ne ya sanar da haka a wani taron manyan ma’aikatan hukumar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na Hukumar Ismail Garba Gwammaja ya fitar kuma ya aikewa manema labarai a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, Kiru ya lura cewa, wadanda ke neman a mika su ga sauran mukamai a jihar na bukatar hukumar ta gayyace su domin samun karin bayani game da takardun gudanar da mulki domin cika bukatun.
“Shugaban ya kuma yabawa gwamnati mai ci bisa yadda take nuna himma wajen zaburar da ma’aikata a daidai lokacin da ya kamata, ya kuma umarce su da su mayar da martani mai kyau don cimma burin da aka sa a gaba,” in ji sanarwar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Sanarwar na cewa babban sakataren hukumar Alhaji Sani Abdullahi Kofar Mata, yana kan ka’idar ma’aikata, ya kuma bukaci daraktocin hukumar da su yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da ayyukansu domin a samu cigaba akan lokaci.