Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna sun duba aikin wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa wanda gwamnatin Kano ke yi a dam din Tiga da Challawa mai ƙarfin wutar lantarki Megawatts 15, inda dam din Tiga zai samar da 7.2 Megawatts sannan na challawa kuma zai samar da sauran.
Haka kuma gwamna Ganduje ya duba wurin tattara wutar wato a Challawa da kuma aikin kwashe wutar daga Tiga zuwa wajen tattara wutar na Challawa.
Idan an kammala aikin wutar, za a yi amfani da ita a gidajen matatar ruwa na Kano da kuma wutar kan titi wato inda za a daina amfani da manyan injina.
Aikin Tiga dam din a yanzu yana kashi 95% ne, kuma ana ƙarasa aikin wanda za a haɗa bututun da ruwan zai shiga domin samar da wurin da kuma dam din inda ruwan zai fito. Akwai bututu guda biyu wanda ɗaya idan ya samar da wutar zai wuce zuwa kogin Kano, sannan ɗayan kuma zai shiga gonaki domin noman rani.
Za a kammala aikin gaba ɗaya nan da wata ɗaya kafin a fara aikin gwaji na wutar.
Gwamna Ganduje na tare da Alhaji Nasiru Aliko Koki, da kwamishinoni da masu bawa gwamna shawara da sauran manyan jami’an gwamnatin.