Gwamnatin jihar Kano ta kwashe akalla almajirai 400 ta maishe zuwa jiharsu na haihuwa wato Katsina a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
A ranar Laraba ne aka karbi almajiran a tsakanin iyakar Katsina da Kano a daidai Gidan Mutum Daya wanda Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya yi.
Inuwa ya yi bayanin cewa almajiran sun fito ne daga kananan hukumomi 23 na jihar Katsina domin neman ilimin addinin Musulunci a shekarun da suka gabata. Sai dai ya tabbbatar da cewa gwamnatin Katsina tuni ta riga ta rufe makarantun tsangaya da na Islamiyyu da maishe da daliban zuwa ga Iyayensu a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Coronavirus.