Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ranar Laraba ya nada attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, da kawunsa, Alhaji Aminu Dantata, da Abdulsamad Rabi’u BUA da Sheikh AbdulWahab Abdullah a matsayin mambobin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar.
Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartaswa ta Jihar Kano da ta sake kafa Hukumar Zakka da Hubsi ta Kano tare da Dokta Ibrahim Mu’azzam Maibushira a matsayin Shugaban Hukumar.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta kuma bayyana sunan Dr AbdulMutallab Ahmed a matsayin kwamishina na daya, Dr Lawi Sheikh Atiq kwamishina na biyu na hukumar.
A cewarsa, sauran mambobin sun hada da wakilan masarautun jihar guda biyar, wakilan ma’aikatar yada labarai, ma’aikatar harkokin addini, Kasuwar Kurmi, Rimi da kasuwannin Singer.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kafa kwamitin tantance kungiyoyin addinin musulunci na duniya tare da Farfesa Sani Zaharaddeen, babban limamin Kano a matsayin shugaba; Dr Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini, mataimakin shugaban kungiyar da Auwalu Shehu Yakasai a matsayin sakatare.