By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Kano ta samarwa da kauyuka biyar na’urar rarraba hasken wutar lantarki a karamar Munjibir karkashin kwamishinan raya karkara da cigaban ta Mr Musa Iliyasu Kwankwaso.
Kwamishinan wanda kuma shine ya kaddamar da shirin yace hakan zai bunkasa tattalin arzikin ma zauna yankunan karkara.
Sanarwar hakan, ta fito ne ta hannun jami’in yada labarai na ma’aikatar Lawan Hamisu -Danhassan inda ya bayyanawa manema labarai, a ranar alhamis ya na mai cewa Musa Iliyasu-Kwankwaso ya kara da cewa garuruwan da suka samu rabauta da wannan shirin sun hadar da Audaran, Gidan Dali, Gidan Tata, Gidan Makera da kuma Gidan Yanhula.
Kazalika kwamishinan yace a yanzu haka ana aikin kafa na’urar rarraba hasken wutar lantarki mai karfin 500kva a Zawaciki dake karamar hukumar Kumbotso inda ake saran kammala aikinta nan da sati daya.
Sannan ya bukaci wadanda suka amfana da shirin dasu kula da kayayyakin kada su barnatar dasu baya da haka su sanar dasu da zarar wata matsala ta faru dan daukar mataki.
Shima a nasa bangaren daraktan hukumar samar da wutar lantarki ga kauyuka Mr Garba Uba-Muhammad ya bukaci gwamnatin jihar da ta karfafa wajen samar da kayayyakin aiki ga mazauna kauyuka.