Maaikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta ware gobe Asabar 5 ga watan Maris 2022, a matsayin Ranar ziyara ga daliban makarantun Firamare da Sikandire na kwana.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Sunusi Saidu Kiru shinee ya sanar da hakan a wata sanarwa, da aka rabata ga manema labarai Mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da jama’a na Maaikatar Aliyu Yusif.
Kwamishinan Ilimin ya kuma yiwa iyaye da yan’uwa fatan gama ziyarar daliban cikin kwanciyar hankali.
Kwamishinan ya kuma Bukaci daukacin wadanda zasu je domin ziyarar, da su kasance masu biyayya ga tsarin Dokokin makarantun da daliban suke.
Yan’uwa da abokan arziki kanyi amfani da wannan dama wajen Kai ziyara ga ‘Ya’yansu da kuma ‘Yan’uwa a wannan rana, tare da ci da kuma sha tare da su domin Sanya Farin ciki a zukatansu.