Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar bayar da duk Wani goyon baya ga Hukumar kidaya t kasa, a yayin da ake Shirin Fara kidayar al’ummar Najeriya, a watan Afrilun sabuwar Shekara Mai shirin kamawa.
Mataimakin gwamanan Dakta Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka a dakin taro na coronation hall dake gidan gwanna fadar Gwamnatin jihar
Da yake jawabi a madadin gwamna dakta Abdullahi Ganduje ya ce ya Zama wajibi ga al’ummar jahar Kano, da su fito tare da bayar da dukkanin goyon bayan da ya dace ga jami’an Hukumar kidaya.
KARANTA ANAN: Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Yobe Ta Ba Da Umarnin Sauyawa Wasu Al’ummomi 2 Matsuguni A Jihar
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ta hanyar haka ne kadai zai saka gwamnati tasan adadin al’ummar ta Domin samun damar samar musu da ayyukan more rayuwa Kamar Samar da tituna, gyaran asibitoci, Samar da makarantu, wutar lantarki, tabbatar da tsaftataccen ruwan sha da sauransu.
Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya ce ko a shekarun da suka gabata al’ummar jahar Kano sun matukar bayar da hadin Kai, Wanda ya Sanya jihar Kano ta Zama ta farko dake da yawan al’umma a Nijeriya.
Shima a nasa bangaren Shugaban Hukumar kidaya ta ƙasa reshen jihar Kano Dr Ismail Lawan suleman ya ce wannan Lokacin zasu gudanar da kidayar ne da na’urori na zamani Domin tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ake so.
A karshe sarkin Gaya Alh Dr Aliyu Ibrahim yaja hankulan al’ummar jahar Kano da Kuma wayanda har yanxu Basu yarda da kidaya iyalansu ba dacewa Wannan ce hanyar su mafi sauki da zasu wadata da duk kafin da gwamnati zatayi wanda zai Kawo cigaba sannan ya Kira da malaman addinai da Kuma limamai dasu taimakawa gwamnati wajen sun cigaba da wayar wa jama’a da hankali Domin sanin mahimmancin abunda ake nufi da kidaya.
A wani labarin kuma: Tinubu Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Kasa – Uba Sani
Dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta a cikin duk ‘yan takarar da ke neman zama shugabannin Najeriya a 2023.
Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya ce Tinubu ya yi yaki kuma ya biya hakkin sa domin dora mulkin dimokuradiyya a kasar nan a yau yayin da sauran ‘yan takarar shugaban kasa suka kasance masu neman gafarar soji kawai.