Gwamantin jihar Kano tace zata cigaba da hada hannu da Kungiyoyi da daidaikun mutane, domin ganin an cigaba da tsaftace jihar baki daya.
Kwaminishinan ma’aikatar muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso shine ya bayyana haka a jiya Juma’a, lokacin da yake rangadi da kuma duba yadda ake kwashe shara a kwaryar birnin jihar Kano.
Kwaminishinan wanda ya samu wakilin babban sakataran ma’aikatar muhallin Malam Adamu Abdu Faragai yaje wuraren zuba shara guda 20 dake kwaryar birni, ya Kuma yi kira ga al’umma dasu cigaba da tallafawa yinkurin gwamantin jihar wajen tsaftace Kano a Koda yaushe.
KARANTA ANAN: Mutane Dubu 700 Ke Kashe Kawunansu Duk Shekara – WHO
Faragai ya Kuma bukaci al’umma dasu guji zuba shara a cikin magudanan ruwan musamman a lokacin aka yin ruwan sama wanda na guda daga cikin abunda yake jayo iftila’in ambaliyar ruwa.
Da yake nasa jawabin a madadin shuwagabanni kungiyoyin cigaban unguwanin Dirmin Iya da kuma Rimin Kira Malam Muktar Isa ya nuna farin sa akan yadda ma’aikatar muhallin ke kwashe sharar akan lokaci ya Kuma yi alkawarin cigaba da bai wa ma’aikatar muhallin hadin Kai ta ko wacce fuska.
A wani labarin kuma: Kaduna 2023: NNPP ta maka INEC Kotu, ta buƙaci soke Takarar Uba Sani
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Jihar Kaduna ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Kotu.
Tana neman a soke Sanata Uba Sani dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin tafka magudi a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022.