Gwamantin jihar Kano ta ce a shirye take wajen kare ɗaliban makarantun jihar tare da malamansu daga kamuwa da cutar Korona, musamman a yanzu da ake dab da buɗe makarantu a jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake ƙaddamar da fara yi wa shugabannin makarantu horarwa a kan yadda za su rinƙa kare kansu daga annobar Korona da ɗalibai.
Sanusi Kiru ya ƙara da cewa wannan horarwa haɗin gwiwa ne da ma’aikatar ilimi da ma’aikatar lafiya da ƙungiyoyi dake taimaka musu, da aka shirya domin fadakar da shugabannin makarantu yadda za su kare kansu da dalibansu da zarar an buɗe makarantu.