Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bayar da gudunmowar kimanin naira biliyan biyu da miliyan biyar domin gina tituna, shingen shinge, samar da wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa ga tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port da aka samar a jihar.
A cewar gwamnatin an samar da su ne domin ganin aikin samar da tashar ya kammala akan lokaci, duba da irin muhimmancin da take da shi.
Mukaddashin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna shine ta bayyana hakan a ranar Juma’a, a lokacin da ministan sufuri Alh. Mu’azu Jaji Sambo ya kai ziyarar gani da ido ofishin tashar ta Dry Port da ke Zawaciki a karamar hukumar Kumbotso.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa gwamnatin Kanon ta tabbatar da cewa aikin ya tabbata ta hanyar samar da yanayi mai kyau domin zai haifar da ci gaban tattalin arziki ba kawai ga Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita ba har ma da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar Kano Hassan Musa Fagge da ya fitar ranar Juma’a.
Gawuna a lokacin da yake karanta jawabin Gwamnan ya ci gaba da cewa Kano ita ce cibiyar kasuwanci da zuba jari a Arewacin Najeriya kuma ita ce mafi girman tattalin arzikin da ba mai da iskar gas ba a kasar, wanda kuma GDP din yankin ya kai kusan dalar Amurka biliyan goma sha biyu wanda hakan ya sa za a iya samun damar masu zuba jari a aikin.
A nasa jawabin Ministan Sufuri, Engr. Jaji Sambo ya ayyana tashar tsandaurin ta Dala a matsayin tashar tsandauri da zata taimaka wajen harkar fito.
Ya kara da cewa Kano gari ne mai tarin masaku da masana’antu da manoma da dama,wanda hakan ya sanya suke buƙatar irin wannan tasha.
A cewarsa an samar da tashar ne a matsayin wani ɓangare na cikin shirin gwamnatin tarayya wajen sake fasalin tashoshin jiragen ruwa da aka tsara domin rage cunkoso tashoshin jiragen ruwa tare da daukar ayyukan sufuri da jiragen ruwa kusa da masu shigo da kaya da masu fitar da kaya a yankin.