Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da yaƙi da zazzabin cizon sauro a ƙarshen kowanne wata har zuwa watan Oktoban shekarar 2020
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan ta cikiin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami’ar yaɗa labaran ma’aikatar Hadiza Namadi.
Ta cikin sanarwar Kwamishinan ya kuma yabawa ma’aikatan lafiya da duk wanda suka yi aikin rabon maganin na kwanaki huɗu da aka kammala a ranar Juma’ar nan.