By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da kudirin gwamnatinsa, na ganin an samar da hukuma ta musamman da zata dinga kula da tituna a jihar baki daya. Da kuma yadda ake gudanar da sufuri.
Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri na kasa wanda ya gudana a jihar Kano. Inda ya ce Hukumar zata duba tsarin yadda ake sufuri da kuma titunan, tare da samar da mafita ga tsarin sufurin kasarnan wanda zai taimaka wajen kawar da tarin kalubalen da bangaren ke fuskanta.
Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dr Nasiru Yusif Gawuna, ya ce Hukumar zata taimaka wajen bunkasa bangaren sufuri, tare da jawo bangarori masu zaman kan su domin zuba hannun jarin su.
Anasa bangaren Ministan Sufuri Mr Rotimi Amechi, ya ce Yanzu haka daftarin sufuri a Nigeria yana karkashin dubawar wasu ɓangarori na kwamitin da aka samar kan tsarin, bisa jagorancin Mataimakin shugaban kasa, kuma suna saka ran cewa za a amince da shi, yayin zaman majalisar Zartarwa gwamnatin tarayya.