A daidai lokacin da aka koma makarantu a faɗin jihar Kano ga ɗaliban da za su zana jarrabawar kammala Sakandire wato WAEC.
Gwamnatin Kano ta sha alwashin korar duk wani shugaban makarantar da ya tsallake dodokin da aka gindaya don kariya daga cutar Korona
Kwamishinan ilimi na jihar Sunusi Ƙiru ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da sashen hausa na BBC.
Ƙiru ya ce b”shakka sai da aka cimma matsaya kafin bawa ɗaliban damar komawa makarantu, kuma ba zamu zuba ido a karya wannan dokar ba”.
Ya ƙara da cewa a matakin da ake a yanzu ya zama wajibi shugabannin makarantun su saka ido don ganin cewa an shawo kan matsalar.
Amincewar komawa makarantun da gwamnatin ta yi ga ɗaliban da suke ajin ƙarshe na babbar sakandire, an fara karatun ne a jiya Litinin.