Yayin da yanayin harkar koyarwa ke kara shiga halin wayyo Allah a Jihar Kano, gwamnatin Jihar karkashin Umar Abdullahi Ganduje ta umarci hukumar kula da ilmin Jihar da ta sauya wa wasu ma’aikata zuwa makarantu don koyarwa.
Umarnin gwamnatin ya ce a yanzu haka ma’aikata kimanin 5000 da suke da kwarewa kan harkar koyarwa.
Wannan na zuwa ne yayin da kwamitin da gwamnatin ta Kano ta kafa kan harkokin ilmi ya yi wani taron gaggawa a Jiya Lahadi tare da mika rahoton da ya tattara.
Ofishin Sakataren gwamnatin Jihar ya ce wadanda ake bukata a halin yanzu su ne masu takardat shaidar koyarwa ta NCE da masu da masu Diploma a harkar koyarwa da dai sauransu.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Lahadi, Kwamishinan yada labaran Jihar Kano Mallam Muhammad Garba ya ce ma’aikatan da za a sauya musu guraben aiki zuwa makarantun za su taso ne daga ma’aikatu da sassan gwamnati gami da ma’aikatan kananan hukumomi, don haka ya bukacesu da su garzaya don bada taimakon su a harkar ilmin jihar.