Gwamnatin Kano ta amince da fitar da kudi Naira Miliyan ɗari biyu da hamsin da bakwai domin biyawa ɗaliban dake karatu a ƙasar Masar kuɗaɗen makarantunsu.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannu sakataren yaɗa labaransa Abba Anwar.
Ta cikin sanarwar ya bayyana cewa za’a biyawa ɗalibai su Arba’in da huɗu kuɗaɗen Alawus-alawus a jami’oin guda biyu dake ƙasar.
A cikin sanarwar ta ce ɗaliban sun rubuta takardar koke kan halin da suke ciki dagane da rashin biya musu kuɗaɗen karautun nasu akan lokaci, wanda hakan sa gwamnati ta amince domin biya musu kuɗaɗen karatun nasu.