Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) domin duba yadda wasu suke yin bahaya a fili barkatai.
Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Ibrahim Ahmad-Sagagi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin da yake kaddamar da rabon magungunan tsaftace hannu da sauran abubuwan da suka shafi lamarin a Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU Ta Mayar Da Martani Ga Adamu Kan Sharhin Biyan Diyya Ga Dalibai
An raba kayayyakin ne ga shugabannin kananan hukumomin jihar masu kula da ruwa, tsaftar muhalli (WASH).
Ahmad-Sagagi, wanda Daraktan Sashen WASH, Alhaji Yahaya Nuhu ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wajen dakile barazanar yin bayan gida a fili saboda yana haifar da munanan kalubalen kiwon lafiya.
Ya bukaci shuwagabannin rukunin WASH na kananan hukumomi 44 da su sanya hannu a kai don magance matsalar.
Kazalika, Wakiliyar UNICEF ta Jihar Kano, Mrs Stella Terve, ta yi kira da a hada kai da ‘yan Najeriya wajen ganin an samu ci gaba, wajen mai da kasar ta zama al’umma a bude ba tare da bayan gida a fili ba.
Ta ce “Jihar Kano ta mayar da hankali wajen kawo karshen dakile lamarin a Kananan hukumomin Danbatta, Garko da Wudil ne
wuraren da ake yin bayan gida a fili barkatai.
“Ta kuma ce za a zabi wasu kananan hukumomi takwas bisa irin wannan dalili; akwai buƙatar ƙoƙarin haɗin gwiwa tare da UNICEF da kuma gwamnatin jihar don duba matsalar.”
Terve ta bayyana cewa yin bayan gida a fili ya zama ruwan dare a yankunan karkara da yawa inda gidaje kalilan ne ke da bandaki.
Ta kara da cewa mutanen na da saurin kamuwa da cututtuka kamar kwalara da kuma cutar amai da gudawa.
NAN